Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafar Libya ya yi murabus – Super Eagles
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasar Libya, Abdelhakim Al-Shalmani, ya yi murabus daga muƙaminsa bayan yasar da tawagar ’yan wasan Super Eagles.
Jaridar The Libya Observer, ta bayyana cewa Al-Shalmani, ya sanar da murabus ɗinsa ne, yayin taron hukumar a ranar Lahadi.
“Ba na son zama ɗaya daga cikin waɗanda za su gaza a harkar wasanni a Libya,” in ji Al-Shalmani.
Ya gode wa abokan aikinsa sannan ya ce ya yafe wa kowa a ɓangaren wasanni.
“Na gode wa dukkanin waɗanda muka yi aiki a hukumar, kuma na yafe wa kowa a ɓangaren wasanni,” in ji shi.
Murabus ɗinsa ya zuwa ne daidai lokacin da tawagar ’yan wasan Super Eagles suka zargi hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya da rashin ba su kyakkyawar kulawa a wasan da za su yi na neman gurbin gasar Kofin Afirka (AFCON) ta 2025.
Tawagar ’yan wasan sun shafe sama da sa’o’i 14 a filin jirgin sama na Al Abraq ba tare da samun wajen kwana ko abinci ba.
Sai dai Aminiya ta ruwaito cewar ’yan wasan sun isa Najeriya, inda suka sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace.
CAF, ta bayyana cewa, “Mun tuntuɓi hukumomin Libya da Najeriya bayan samun labarin cewa tawagar Najeriya da ma’aikatansu sun maƙale a wani yanayi mara daɗi.
“An miƙa lamarin ga Hukumar Ladabtarwa ta CAF don gudanar da bincike, kuma za a ɗauki matakin da ya dace a kan waɗanda suka karya dokokin CAF.”
Source: Aminiya