Yadda Hisbah ta kama Kwamishinan Jigawa da matar aure a Kano
Jami’an hukumar Hisbah a Kano sun kama Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara, bisa zargin yin lalata da wata matar aure.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa wanda ake zargin ya shiga hannu nr ne bayan mijin matar ya kai rahoto ga Hisbah yana zargin kwamishinan da yin alaka da matarsa.
Wata majiya a hukumar Hisbah wanda ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa DAILY NIGERIAN cewa wanda ake zargin har yanzu yana tsare a shelkwatar Hisbah dake Kano.
Majiyar ta kara da cewa bayan samun rahoton, Hisbah ta tura tawagarta ta leken asiri don bin diddigin wadanda ake zargin don tabbatar da gaskiyar batun.
“Mun dauki lokaci muna bin diddigin wadanda ake zargin har sai jiya (Alhamis) da daddare, kimanin karfe 10:00 na dare, lokacin da muka hango wanda ake zargi da matar suna shiga wani gini da ba a kammala ba wanda yake mallakin shi.
“Da muka karasa wajen ginin, mun buga kofar, wanda wani mai gadi ya ke tsare da wajen. Da muka ci gaba da buga kofar, wanda ake zargin da kansa ya fito don ganin suwaye ke kofar.
“Da ya bude kofar, muna tare da mijinta wanda ya shigar da karar kuma ya gan ta a cikin mota,” inji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa da ta ga mijinta tare da jami’an Hisbah, sai ta firgita kuma ta yi kokarin tserewa a cikin motar, inda ta cire kyauren gidan amma tana fita waje ta tarar da motar Hisbah ta toshe kofar wucewa.
Majiyar ta ce kwamishinan ya amsa laifin yin lalata da matar har sau uku.
Majiyar ta kara da cewa an tsare su biyun a shelkwatar Hisbah kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
Da aka tuntubi Mataimakin Kwamandan Hisbah, Mujahid Aminuddeen, domin jin ta bakinsa, bai amsa wayar wakilinmu ba kuma bai mayar da sakon kar ta kwana ba wajen bada amsa kan lamarin.
Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan ya fitar a yau Asabar ya musanta zargin cewa an kama shi yana lalata da matar aure, inda yayi barazanar kai batun gaban kotu.
A halin yanzu kuma, Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya sanar da dakatar da kwamishinan har sai an kammala bincike.