Labaran Hausa

Wani Zaki Ya Kashe Mai Kula Da Shi A Gonar Obasanjo

Ana fargabar cewa wani Zaki ya kashe ɗaya daga cikin masu kula da shi a cibiyar ajiye namun dawa ta tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da ke birnin Abeokuta a Jihar Ogun.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar, inda Zakin ya yi wasan kura da mutumin, Babaji Daule mai shekaru 35 wanda a dalilin haka ya ce ga garinku nan.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa babban jami’in tsaro a Gandun Adana Namun Dawar na Obasanjo ya sanar da su.

Sai dai kakakin ’yan sandan ya ce tsautsayi da ba ya wuce ranarsa ne ya sanya  mutumin da lamarin ya rutsa da shi ya yi sakacin barin sakatar da ke killace Zakin a cikin keji bayan ya bai wa namun dawar abinci.

Ya ce wannan lamari ne ya bai wa Zakin damar fitowa kuma ya far wa mai kula da shi, inda ya ji masa rauni a wuya kuma a dalilin haka ajali ya katse masa hanzari.

Ya ƙara da cewa, an ajiye da gawar mutumin a ɗakin killace gawarwaki da ke Babban Asibitin Ijaye.

Source: Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button